3 John

1Wasiƙa daga Dattijon nan,

Zuwa ga ƙaunataccen abokina Gayus, wanda nake ƙauna da gaske.

2Abokina ƙaunatacce, ina adduʼa ka sami zaman lafiya domin kome yǎ yi maka daidai, kamar yadda ruhunka yake zaune lafiya. 3Na yi farin ciki ƙwarai saʼad da waɗansu ʼyanʼuwa suka zo suka kuma yi zance game da yadda kake da aminci ga gaskiyan nan da kuma yadda kake cin gaba cikin gaskiyan nan. 4Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ʼyaʼyana suna cikin gaskiyan nan.

5Abokina ƙaunatacce, kana da aminci cikin abin da kake yi wa ʼyanʼuwa, ko da yake su baƙi ne a gare ka. 6Sun faɗa wa ikkilisiya game da ƙaunarka. Za ka kyauta in ka sallame su a hanyar da ta cancanci Allah. 7Saboda Sunan nan ne suka fito, ba sa karɓan wani taimako daga waɗanda ba masu bi ba. 8Saboda haka ya kamata mu nuna halin karɓan baƙi ga irin mutanen nan domin mu yi aiki tare saboda gaskiyan nan.

9Na rubuta wa ikkilisiya, amma Diyotarifes, wanda yake son zama na farko, ya ƙi yǎ yi hulda da mu. 10Saboda haka in na zo, zan tone abin da yake yi, yana gulmar ƙeta game da mu. Wannan ma bai ishe shi ba, har yana ƙin marabtar ʼyanʼuwa. Yana kuma hana waɗanda suke so yin haka yana ma korinsu daga ikkilisiya.

11Abokina ƙaunatacce, kada ka yi koyi da abin da yake mugu sai dai abin da yake nagari. Duk mai yin abin da yake nagari daga Allah yake. Duk mai yin abin da yake mugu bai taɓa ganin Allah ba. 12Demetiriyus yana da shaida mai kyau daga wurin kowa-har gaskiya kanta ma ta shaide shi. Mu ma muna ba da shaida mai kyau a kansa, ka kuma san cewa shaidarmu gaskiya ce.

13Ina da abubuwa da dama da zan rubuta maka, sai dai ba na so in yi amfani da alƙalami da inki in rubuta su. 14Ina fata in ganka nan ba da daɗewa ba, za mu kuwa yi magana fuska da fuska.

15Salama gare ka. Abokai a nan suna gaishe ka. Ka gai da abokai a can da sunansu.

Copyright information for HauSRK